1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Ziyarar Fafaroma Francis

January 31, 2023

Fafaroma Francis na biyu ba zai iya magance rikice-rikice cikin sauki ta hanyar sakon neman zaman lafiya ba, amma watakila zai iya karfafa fahimtar juna tsakanin al'ummar kasar.

https://p.dw.com/p/4MuxU
Vatikan | Fafaroma Francis | Katolika
Jagoran mabiya darikar Katolika na duniya, Fafaroma FrancisHoto: FILIPPO MONTEFORTE/AFP

Har yanzu, ba kowa ake bari ya shiga garin Ndolo ba. A kofar shiga filin jirgin saman cikin gida na garin, sojoji na barin matafiya ne kawai da manyan motoci da ke dauke da katako da karafa su shiga. Ana bukatar wadannan domin gina wurin da za a yi taron addu'a. A nan ne Fafaroma Francis zai gudanar da taro na gagarumar addu'a ga jama'ar Kinshasa, wadda babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango suka dade suna jira. Mai shekaru 86 yanzu,  FaFaroma Francis ya dage tafiyar har tsawon watanni shida saboda dalilai na rashin lafiya. Shekaru 37 da suka gabata ne dai, Fafaroma John Paul II ya kai ziyara Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Ya yin ziyarar tasa, ya gana da Mobutu Sese Seko. A wancan lokacin kamar yadda yake a yanzu, Kinshasa birni ne mai ban sha'awa da ya shahara da yawan mashaya da kidan rumba da kuma baje kolin arziki. Amma kuma akasin hakan shi ne, babban birni ne wanda ke dauke da kusan mutane miliyan 15 da mafi yawansu ke rayuwa cikin talauci. A gabashin kasar, mutane sukan ji cewar babban birninsu ya yi watsi da su.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | M23 | Tawaye | Rikici | Gudun Hijira
Daruruwan mutane a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, na cikin halin taskuHoto: Nicholas Kajoba/Xinhua/IMAGO

Tun bayan faduwar gwamnatin Mobutu a shekarun 1990, zaman lafiya bai dawo a wurare da dama ba. Tsakanin 1998 zuwa 2007 kadai, mutane miliyan biyar da dubu 400 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen hankula ko saboda dalilan da rashin jin kai da ya haifar a cewar wani bincike da kungiyar agaji ta kasa da kasa ta yi. Fafaroman zai zo Kwango da sakon zaman lafiya, in ji jakadan Vatican a kasar Ettore Balestrero. A cikin 2020, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce akwai sama da kungiyoyin 'yan tawaye 120 a gabashin kasar. Guda daga cikin kungiyoyin ita ce kungiyar M23 da ta sake farfado da kai farmaki a kusa da Goma a baya-bayan nan, inda ta sake haifar da rikici tsakanin Kwango da Rwanda da ke makwwabtaka. Hakan ya faru ne saboda makwabciyar kasar tana goyon bayan 'yan tawayen, kamar yadda kwararrun Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar. Kwango tana daya daga cikin kasashen duniya da ke da mafi yawan mabiya darikar Katolika, inda kididdigar da fadar Vatican ta yi ta nunar da cewa sama da mutane miliyan 52 ko ma kusan rabin al'ummar kasar mabiya darikar ne.