Wani Fada ya yi wa wata fyade a Indiya
March 2, 2016Wata kotu a kasar Indiya ta yanke hukuncin shekaru 40 a gidan kaso ga wani babban malamin majami'a saboda laifin aikata lalata da wata karamar yarinya ‘yar shekaru 12 kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana a ranar Laraban nan.
Sanil K. James an gabatar da shi a gaban kotu a shekarar 2014 bayan gano wannan aikin cin amana da ya yi a wata coci mai suna Salvation Army church wacce ke a Kudancin jihar Kerala.
Har ila yau wannan fada ana kuma zarginsa da aikata lalata da wata yarinyar baya ga wacce aka gabatar da shi a gaban kotu a kanta a wancan lokaci, kamar yadda Pious Mathew me gabatar da karar ke fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP. A cewar Mathew wannan fada ya dauki tsawon watanni biyu yana lalata da yarinyar wacce ke shekaru 13 a yanzu a cikiin cocinsa.
Kamar yadda hukumar da ke lura da aikata irin wadannan miyagun laifuka a kasar ta Indiya ta bayyana fiye da yara 18,000 ne a ka aikata musu wannan laifi a kasar a shekarar ta 2014, abin da kuma ke faruwa bayan yaran sun aminta da mazambatan.