Cutar corona na ta'azzara a wasu yankuna
March 10, 2021Talla
Hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta sanar da cimma yarjejeniyar sayen karin alluran rigakafin corona miliyan hudu daga kamfanin Pfizer-BioNtech, wa wakilan kasashe 27 da ke kungiyar, domin dakile ta'azzarar cutar a wasu yankuna.
Samun alluran zai taimaka wajen bude kan iyakokin da a yanzu haka ke rufe, ga harkokin kasuwanci da ma zirga zirgan mutane. Kungiyar ta EU dai ta sanar da sunayen yankuna da cutar ke kara ta'azzara kamar Tyrol a Australiya, sai Nice da Moselle a Faransa, Bolzano a Italiya da wasu garuruwan Bavaria sa Saxony a nan tarayyar Jamus.