EU: Ministoci za su gana bayan harin Brussels
March 23, 2016Talla
Ministoci na cikin gida da na shari'a daga kungiyar Tarayyar Turai za su yi wani zama a ranar Alhamis a birnin Brussels na Beljiyam, abin da ke zuwa bayan kai harin da ya yi sanadi na rayukan mutane 31 kamar yadda jami'ai daga kungiyar ta EU suka bayyana a ranar Laraban nan.
Kasar Holland wacce ita ke jan ragamar wannan kungiya a mulkin da a ke na karba-karba, a sakon da ta fitar na Twitter ta ce taron zai hada ministocin na shari'a da na tsaro da wakilai daga ma'aikatu daga Kungiyar ta EU.