Libiya: EU ta hana sayar da makamai
February 17, 2020Talla
Ministan harkokin kasashen waje na Jamus Heiko Maas ne ya bayyana hakan, inda ya ce ministocin harkokin kasashen ketare na kasashe mabobin kungiyar 27 sun amince da wannan matakin, yayin wani taro da suka gudanar a Brussels babban birnin kasar Beljiyam. A cewar Maas ba wai za a sanya idanu a kan dokar haramta sayar da makaman ta hanyar amfani da na'urar satellites kawai ba, za ma a sanya idanun ta hanyar amfani da jiragen ruwa a Tekun Bahar Rum. Rahotanni sun bayyana cewa za kuma a kawo karshen rundunar sintirin gabar Tekun Bahar Rum din ta hadin gwiwar kasashen Turai ta "Sophia".