Emirates zai dakatar da aiki a Najeriya
August 18, 2022Kamfanin jiragen sama na Emirates na Hadaddiyar Daula Larabawa da ke da mazauni a birnin Dubai ya sanar da cewa, zai dakatar da aikin jigilar fasinja daga Najeriya kama daga watan Satumba mai zuwa. A cikin sanarwar kamfanin ya ce, ya dauki matakin ne don yadda ya kasa fitar da kudadensa daga kasar da kuma rage yawan asarar da ya ke tafkawa a sakamakon matsaloli masu nasaba da faduwar darajar naira a kasuwannin duniya, tun bayan da gwamnatin Najeriyar ta dage kan sai an siyi tikitin jirgin Emirates da takardar kudin naira.
Tun daga watan Agustan 2021 gwamnatin Najeriyar ta hana yin hada-hadar canjin kudaden waje a kasar baya ga dalar Amirka, lamarin da ya haifar da nakassu ga kananan 'yan kasuwa da masu zuba jari. Dubai na daya daga cikin biranen da 'yan kasuwar Najeriya dama masu son shakatawa ke yawan zuwa.