Emirates zai ci gaba da jigilar fasinja a Najeriya
September 1, 2022Kama daga kamfanin Delta Airlines na kasar Amirka ya zuwa Emirates na Hadaddiyar Daular Larabawa ko bayan South African Airlines na Afirka ta Kudu dai, sannu a hankali kamfunan sufurin sama na kasashen waje dai na barazanar dakatar da ayyukansu a cikin Najeriya bisa rashin kudade na waje da suke da bukata daga cinikin tikiti.
Sama da dalar Amirka miliyan 600 ne dai kamfunan suka ce sun makale a bankunan Najeriya, lamarin da ya sanya su barazanar tsayar da jigilar fasinja daga ketare zuwa kasar idan dai ba biya musu bukatunsu ba.
Tun da farko kamfanin Emirates dai ya ce tun daga Alhamis din nan zai tsayar da ayyuka a yayin da dan uwansa na Delta ya tsara ficewa cikin watan gobe na Oktoba.To sai dai kuma tun ba a kai ga ko'ina ba kamfunan sun fara lashe amai, inda Emirates ya sauya taku; tare da janye aniyarsa da kuma sanar da ci gaba a cikin kasuwar sufurin saman Najeriya kasar mai tasiri. Kamfanin ya ce zai ci gaba da aiki daga birnin Lagos da ke zaman kasuwa mafi tasiri a kasar.
Kwanga-gaba-kwan-baya da Emirates din ke yi dai tuni ta fusata hukumomin Najeriya. Ministan sufurin saman kasar Hadi Sirika ya ce kamfunan sufurin ketare na da zabin zama cikin kasar ko kuma ficewa.
''Motsi kadan sai ka ji Emirates ya ce zai daina zuwa Najeriya, duk da muna da bukatarsu, ai ba su kadai ba ne.'' in ji ministan.
Tarrayar Najeriya dai na zaman kasa ta kan gaba a nahiyar Afirka ga batun fasinjoji na sama, inda a bara kadai aka kiyasta sama da mutane miliyan 15 suka hau jirgin sama walau ciki ko kuma fita zuwa wajen kasar.
Kyaftin Bala Jibril da ke sharhi bisa harkar sufurin sama a Abuja ya ce Najeriyar na da tasirin da kamar wuya kamfanonin ketare su kawar da idanunsu daga gare ta.