Adawa da zaben fitar da gwani a Ekiti
January 28, 2022Za dai a gudanar da zaben gwamna a jihar ta Ekiti ne, a ranar 18 ga watan Yunin wannan shekara. Biodun Oyebanji ne dai ya lashe zaben na APC, yayin da Opeyemi Bamidele ke biye maa a matsayin na biyu. A jami'yyar PDP mai adawa kuwa Mr. Bisi Kolawole da tsohon gwamnan jihar Ekitin Ayo Fayose ke marawa baya ne ya lashe zaben, inda tsohon gwmna a jihar Mr Segun Oni ya zo na biyu. Sai dai suma a nasu bangaren, 'ya'yan jam'iyyar ta PDP sun yi fatali da sakamakon zaben nan take. Tun bayan kammala zaben n a fitar da gwani dai, manyan 'ya'yan jam'iyyar ta APC da suka sanya ido suka bar jihar, a hannu guda kuma 'yan takarkarun jam'iyyun biyu a yayin zaben na fitar da gwani sun zuba ido suga matakin da iyayen jam'iyyun biyu za su dauka a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar dangane da sakamkon zaben da kuma rikita-rikitar da ta biyo baya.