Ebola ta sake bulla a kasar Saliyo
January 21, 2016A ranar Alhamis din nan jami'ai a kasar Saliyo sun tabbatar da wani sabon lamari na cutar Ebola a kasar, karo na biyu tun bayan da kasashen yammacin Afirka suka yi bikin kawo karshen cutar a makon da ya gabata. Sake bullar cutar ya tilasta wa kasar sake bude cibiyoyin kula da masu jinyar cutar ta Ebola sannan ta kaddamar da tsarin binciken lafiyar al'umma ciki har da kakkafa shingayen tsare ababan hawa a kan manayan hanyoyin kasar. Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ce gwaggon Marie-Jallo 'yar shekaru 22 din nan da ta mutu sakamakon Ebola a ranar 12 ga watan nan na Janeru, ita ce ta nuna alamun kamuwa da cutar. Ita dai matar 'yar shekaru 38 ta kasance mai kula da Marie-Jallo lokacin da take jinya. Yanzu haka an garzaya da ita wani kebabben wuri kuma ana sa ido kanta. Yanzu haka dai an gano mutum 150 da suka yi mu'amala da Marie-Jallo kuma 42 daga cikinsu na cikin babban hatsarin kamuwa da cutar, inji jami'an WHO.