Cutar Ebola na daf da zama tarihi
July 31, 2015Wata allurar gwaji kan cutar Ebola da aka gwada kan wasu dubban al'umma a kasar Gini, alamun farko na gwajin cutar na nuna cewa allurar tana aiki wanda hakan ana sa rai zai taimaka wajen kawo karshen wannan cuta a Yammacin Afirka kamar yadda sakamakon binciken ya nunar a ranar Juma'an nan.
Ya zuwa yanzu dai babu wata allura mai lasisi da aka amince tana maganin cutar Ebola wacce ta kashe sama da mutane 11, 000 a Yammacin Afirka. Kisan da ke zama mafi yawa a tarihin cutar a duniya.
Cutar dai na ci gaba da samun koma baya sannu a hankali cikin wadannan watanni a kasashe biyu da suka fi cutawa da wannan annoba wato kasashen Saliyo da Laberiya.
Idan har aka tabbatar da ingancin wannan allura ta gwajin maganin cutar ta Ebola, lamarin zai iya zama mabudi ga sabon babin yaki da cutar ta Ebola kamar yadda Dr. Margaret Chan darakta a Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta shirya wannan bincike ta bayyana.