1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ebola na kara lakume rayuka a Afirka

August 23, 2014

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce yawan wadanda cutar Ebola ta hallaka a yammacin Afirka na dada karuwa biyo bayan samun rahoton mutuwar karin mutane 77 .

https://p.dw.com/p/1CzeV
Hoto: Carl De Souza/AFP/Getty Images

Hukumar ta ce mutanen da suka mutun sun kasance 'yan kasashen Saliyo da Guinea da Laberiya da kuma Najeriya wanda ta ce hakan ya kawo adadin wadanda cutar ta hallaka zuwa 1,427 . Hukumar wadda ke da shalkwata a birnin Geneva ta nunar da cewa kawo yanzu akwai rahotanni bullar cutar na wadanda aka tabbatar suna dauke da Ebolan da kuma wadanda ake gudanar da bincike a kansu har 2,615 a wanna yankin. Hukumar ta kuma bayyana fargabar cewa yawan mutanen da suka mutu ko kuma suke dauke da kwayar cutar ta Ebola sunfi haka. Ta kara da cewa wasu na boye 'yan uwansu da ke dauke da cutar ganin cewa ba ta da magani inda suke gwammacewa mutanen su mutu a gidajensu. Hukumar ta WHO ta kara da cewa anfi fuskantar wannan matsalar a kasar Laberiya inda mutane ke nuna kyama da kuma kyarar masu dauke da kwayar cutar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba