Ebola na ci gaba da lakume rayuka
August 15, 2014Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta sanar da cewa adadin wadanda cutar Ebola ta lakume rayukansu a yammacin Afirka na karuwa. Kiyasin da hukumar ta WHO ta fitar na nuni da cewa kawo yanzu mutane sama da 1100 ne cutar ta Ebola ta hallaka a yankin yammacin Afirka sakamakon rahoton karin mutuwar wasu mutane 74 da aka samu tsakanin 12 da 13 ga wanna wata na Agusta da muke ciki a kasashe hudun da ke fama da cutar. Kiyasin na hukumar ta WHO ya kuma nunar da cewa an samu sababbin rahotannin bullar cutar har sama da 150 a kasashen Gini da Laberiya da Saliyo da kuma Najeriya wanda ya kawo adadin wadanda ke dauke da cutar a yanzu haka zuwa 2,127 a tssakanin kasashen hudu. Yanzu haka dai akwai fargaba mai tsanani ta barkewar yunwa a Laberiya sakamakon wannan bala'i na annobar cutar Ebola.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu