Ebola a Saliyo-Kokarin shawon kan cutar
Fiye da mutane 1,500 suka kamu da cutar Ebola a Saliyo. 'Yan Saliyo suna ci gaba da samun kwarin gwiwar yaki da cutar; wasu kan samu kwarin gwiwa daga al'umma.
Rayuwa tana gudana duk da Ebola
Suard Demby (a dama) tana ci gaba da sayar da farfesu a babbar kasuwar kayan lambu da ke Freetown babban birnin Saliyo. 'Yar shekaru 19 da haihuwa tana cike da tsoron yuwuwar kamuwa da Ebola a cikin cikowar mutane, amma ba ta da damar kaucewa aikin. Iyalanta suna dogara a kan kudin da take samowa.
Mai zane ya shiga yaki da Ebola
Ana bukatar wuraren da ake kebe wadanda suka kamu da cutar domin yi musu magani a duk fadin Saliyo. Amma akwai karancin ma'aikata da wuraren da suka dace. Kamara, masanin zanen fasalin gidaje, ya yi watsi da aikin da yake yi, saboda ya taimaka a gina wajen kebe mutanen da suka kamu da Ebola a birnin Freetown. Za a fara aiki da wurin a 'yan makonni masu zuwa.
'Yan sanda suna gadin gawa
Ba ta bayyana mana sunanta ba, amma mutanen yankin na kiranta 'Mama G.' Mafi yawa suna daukar 'yar sandan a matsayin uwa wadda take daukar lokaci wajen sauraron damuwa da tsoron da mutane ke da shi. A makonni uku da suka gabata, ta yi rakiyar gawarwakin wadanda Ebola ta hallaka zuwa binnewa. Aikin da ya jefa ta a matsala, kamar yadda ta ce.
Ban zan fice daga Saliyo ba
Ole Hengelbrock dan kasar Jamus ya isa Freetown fiye da shekara guda da ta gabata domin aiki da wani shirin taimakon yaran da ke kan tituna, tare da wata kungiyar ba da agaji ta Cap Anamur. Saliyo yanzu ta zama masa gida na biyu kuma yana buga wasan Premier Lig na kasar. Ba ya daukan Ebola a matsayin wani rikicin da zai sanya ya koma Jamus.
'Yan aikin sa kai sun saka kayan kariya
Wannan shi ne karon farko da Momudo Lambo ya saka kayan kariya. yana cikin masu samun horo na aikin sa kai da ke shirin shiga wajen da ake kulawa da masu dauke da cutar Ebola. Aiki mai hadari amma "a lokaci mai wuya, abu ne kawai da ya kamata a yi". a cewar dan shekaru 28 da haihuwa.
Ilimin Ebola
Ilmantar da mutane kan cutar ya zama mataki mafi inganci na tsayar da yaduwar cutar, a cewar Usman Rahim Bah. Yana kashe kudinsa wajen tattara bayanai a kan cutar Ebola, kuma ya shafe makonni yana bi gida-gida domin yada bayanan da suka hada da tsafta da kare lafiyar al'umma.
Ko yaushe a bakin aiki
Stella ta shafe kimanin shekaru 30 tana aikin jinya, kuma ta ga abubuwa masu yawa da suka faru a asibiti, amma babu kamar wannan rikicin. Lokacin da aka fara ruwaito cutar Ebola, mafi yawan abokan aiki sun bar asibitin amma ita ta tsaya a bakin aiki, kuma tana da yakinin cewa kasar za ta shawo kan bala'in.
Hadari ba shi da nisa kwata-kwata
Desmond Reez shine shugaban kungiyar ba da agaji ta Red Cross. Ya dauki nauyin tabbatar da kare lafiyar ma'aikatansa wadanda ke daukan gawarwakin masu Ebola kullum. 'Na san cewa muna da horon kariya.' a cewarsa. Amma kullum yana fata wannan bala'i ya kawo karshe.