Taron DW na 'yan jaridu na shekara
June 14, 2021Taken taron na shekara ta 2021 shi ne cikas da ake fuskanta na kirkire-kirkire, kuma sakamakon annobar cutar coronavirus ba duk mahalarta taron suka hallara a birnin Bonn kamar yadda aka saba ba. Sai dai ana amfani da kafar Internet wajen tattaunawa da mahalarta daga bangarori dabam-dabam na rayuwa. Babban abin da aka mayar da hankali shi ne kalubalen kirkire-kirkire da damar da za a samu kan samar da ci-gaba. Taron na 'yan jaridu na zuwa ne shekara guda, bayan kusan rufe daukacin harkokin rayuwa a kasashen duniya sakamakon bullar annobar cutar coronavirus wadda ta halaka milyoyin mutane a duniya. Sai dai sannu a hankali cutar tana lafawa bayan samun allurar rigakafi, gami da matakai masu tsauri da aka dauka a kasashen dabam-dabam na duniya.
Karin Bayani: Taron shekara-shekara da tashar DW ke yi
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na cikin mahalarta taron na bana, wadda ta yi jawabi ta bidiyon da aka nada tare da nuna tasirin 'yancin mutane: "'Yanci, wani abu ne wanda yake da tasiri ga harkar zamani da na Internet. Kafofin zamani sun kawar da iyaka, inda mutane daga kasashe dabam-dabam da al'adu mabambanta suke haduwa. Haka ya samar da dama ga mutune wajen kara fadada tunaninsu. Kafar intanet ta samar da damar tattaunawa ga mutane domin a ji daga gare su."
Tobore Ovuorie da ta samu lambar yabo ta tashar DW kan binciken kwakwaf da ta yi domin gano hanyar wayar da kan mutane sakamakon matsalar safarar murtane da ake fuskanta a Najeriya, na cikin mahalarta taron: "Na rasa na kusa da ni saboda safarar mutane, ban samu damar magana da ita ba kafin faruwar lamarin. Sannan na kara rasa wasu na kusa da ni matasan 'yan mata, wannan ya fusata zuciyata."
Karin Bayani: Taron 'yan jaridu na Global Media Forum na 2017
Wannan binciken da Tobore Ovuorie 'yar shekara 33 ta yi, ya janyo ta shahara. A cewar Peter Limbourg shugaban tashar DW, aikin ba abu ne mai sauki ba: "Za a iya cewa ya kawo haske ga mutanen da suke cikin duhu, ina tsammani wannan mace ce mai jajicewa, kuma ta cancanci yabo ba ga aikin tukuru ba kadai, har saboda kalubalen da ta fuskanta lokacin aikin."
Taron na Global Medeia Forum na DW kamar yadda aka saba, zai duba duk matasaloli da kablubalen abubuwa da aka tattauna domin samun mafita da karin hanyoyin inganta kafar yada labarai a yanayi mai tsauri da duniya ta samu kanta.