1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubun wasu 'yan Siriya ya cika a Jamus

Abdul-raheem Hassan
November 21, 2017

Hukumomin tsaro a kasar Jamus sun tabbatar da kama mutane shida kan alaka da kungiyar I S, ana zargin matasan na shirin kitsa kai hare-hare a birane hudu na kasar.

https://p.dw.com/p/2nzlV
Deutschland Symbolbild SEK
Hoto: Getty Images/S. Steinbach

Dubun 'yan Siriyar ya cika ne bayan da 'yan sanda 500 suka yi dirar mikiya a wani somame na musamman a gidaje takwas da a ke zargin masatan na kimtsa kai hari a biranen hudu da ke fadin kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matasa hudu cikin wadan da aka kama, sun shigo Jamus a shekarar 2014 a matsayin 'yan gudun hijira, ya yin da sauran biyun sun shigo kasar a shekarar 2016. 

Dan sanda mai gabatar da kara a birnin Frankfurt, ya ce wadan da ake zargi, ba su kai ga kaddamar da hare-haren ba amma an gano sun kammala dukkannin shirin tarwatsa manyan wurare ciki har da kasuwar kirsimeti.

Jaridar Jamus the Welt, ta ruwaito cewa 'yan sanda sun yi awon gaba da komfutoci da wayoyin hannu hada da wasu muhiman takardu a yayin kai somame kan wadan da ake zargin a ranar Talata.