Dubban mutane na tsere wa rikicin Boko Haram
September 9, 2014A daidai lokacin da jami'an tsaron Najeriya ke ci gaba da gwabza fada da ‘yan Kungiyar Boko Haram domin karbe ikon wuraren da suka kubuce wa hukumomin Najeriya, dubban 'yan gubun hijira na ci gaba da kwarara zuwa manyan birane inda suke cikin mummunan hali na karancin abinci da magunguna.
Yanzu haka dai Kungiyar Boko Haram ta karbe garuruwa sama 10 a jihohin Borno da Yobe da Adamawa wanda ke karkashin dokar ta baci sama da shekara guda, abin da ya haifar da tserewar mutanen yankunan zuwa wuraren da suke ganin tudun na tsira ne.
A iya cewa yawancin mutane wadannan garuruwa da aka kwace musamman mazansu sun fice daga garuruwa saboda fargaba da rashin sanin abin da ka iya faruwa da su in sun tsaya ganin an hallaka 'yan uwansu.
Yawancin wadanda suka tseren na shiga makobtan kasashe na Kamaru da Nijar da kuma manyan biranen na yankin arewacin Najeriya domin tsira daga wadannan hare-hare da ke rutsawa da su, wani lokaci har da jami'an tsaro.
Mawuyacin hali da hatsarin kamuwa da cututtuka
Akwai da dama da suka samu mafaka a gidajen 'yan uwa da abokan arziki a garuruwan Maiduguri da Yola da da Damaturu da Gombe, inda wasunsu kuma ke zaune a wasu sansanonin 'yan gudun hijira da jihohin makobta suka tanadar.
To sai dai da yawa daga cikinsu ba su samu wuraren da za su kwana ba, inda da yawansu ke kwana karkashin bishiyoyi da wurare marasa tsabta tare da fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka.
Ga ma abin da wani daga cikinsu wanda ke da zama a Maiduguri ya nunar.
"Yanzu haka gaskiya idan ka je daga abin da ya kama daga tashar Bama har wajen Welcome to University za ka samu mutane suna kwance a gindin bishiya, wasu ba su da lafiya suna kwance ba abinci, ba ruwa, ba wani dauki, ba wani magani, ba komai, mutane suna zube kara zube a wannan wuri. A wannan Area kam ba abin da muka gani."
Gwamnatoci na cewa suna bakin kokarin sun tallafa wa 'yan gudun hijirar, amma har yanzu dubbansu suna cikin halin ni 'ya su.
Daukar matakin kare kai
Ko wane hali al'ummar wannan yanki ke ciki? Muhammadu mai kayan miya Orji Kwatas Gombe ya ba da amsa kamar haka.
"Ai mu talakawan arewa maso gabasin Najeriya mun daina barci tun ba yau ba sakamakon rashin tsaro da fargaba da mu ke ciki a kullum, saboda shugabanninmu sun kasa kare mu da dukiyoyinmu baki daya. Yanzu ka duba 'yan gudun hijirar da suke Gombe sun fi bila adadin, kullum suna kuka sakamakon rashin tsaro da barin garuruwansu da suka yi a halin yanzu. Abin da ya rage mana shi ne ya kamata kowa ya tashi ya kare kansa, saboda ba za mu tsaya muna gudu daga mu har jami'an tsaro ba. Duk mun zama abu daya kenan, kai da baka ko kwari da baka ga Soja ma yana gudu ai ka ga abu ya gama lalace kenan. Saboda haka ni dai kira na kowa ya tashi ya kare kansa kuma Allah Ya kare mu."
Yanzu haka babu alkalumma na yawan 'yan gudun hijirar saboda yadda suke kwarara zuwa birane. Lamarin dai na haifar da fargaba na halin da za su iya kasancewa nan gaba in ba su samu taimako ba.
Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin hukumar bada agajin gaggawa mai kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ya ci tura.
To sai dai bayanai da ke fitowa daga Maiduguri ya nuna gwamnatin jihar Borno ta bude wasu cibiyoyin kula da marasa lafiya na tafi da gidanka da kuma tura taimakon abinci da ruwan sha amma dai har yanzu wasu wuraren ba su san ana yi ba.