1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Jama'a na tserewa daga yankin Ambazonia

August 29, 2019

Kimanin mutum 10,000 da suka hada da mata da kananan yara suka tsere daga yankin Kamaru mai fama da rikici bayan da ‘yan aware suka yi kiran gudanar da gagarumar zanga zanga inda ake fargabar tashin hankali

https://p.dw.com/p/3OiN4
Grenze Tschad - Kamerun 2015 | N'Gueli-Brücke
Hoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes

Wannan lamari dai na zuwa ne sakamakon karuwar zaman dar-dar da ake ciki a 'yan kwanakin nan. Tun a karshen makon da ya gabata jama‘a ke kaurace wa yankunan Bamenda da Buea zuwa wasu sassan Kamaru musamman garuruwan Yaounde da Douala dama Bafousam.

Dalilin hijirar mutanen dai shi ne fargabar da suke yi na yiwuwar fuskantar farmaki daga bangaren ‘yan aware  bayan hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran tawayen Julius Ayuk Tabe a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Kamerun Afrika
Cikin garin Yaounde a kasar KamaruHoto: picture alliance/Bildagentur online

Daya daga cikin wadanda suka yi nasarar ficewa ita ce Celine Tanui tare da ‘ya’yanta uku wadanda take son idan ta isa garin Bafousam, ta sanya su a makaranta saboda jimawar da suka yi ba tare da karatu ba a yankin da suka yi kaura.

A yanzu dai kamfanonin sufuri da ke yankin sun ninka kudin da suke karba na mota. Lamarin kuma ya zo daidai lokacin da mahukntan kasar Kamarun suka ja damarar ganin an sake bude makarantun yankin a farkon watan Satumba bayan daukar kusan shekaru uku suna rufe.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Masu zanga zanga a yankin Bamenda a KamaruHoto: Getty Images/AFP

Gwamnatin Kamaru dai ta ce ‘yan awaren sun rufe makarantun firamare  sama da dubu hudu daga cikin 5300 da ake da su a yankin, kamar yadda ministan sadawa a kasar Rene Emmanuel Sadi ya shaida wa mana.

A takaice baki dayan ta’asar da ‘yan aware suka yi wa ilimi a wannan shiya, ta fi karfin abin da hankali zai iya tunawa. Rashin hankali ne yin haka. Babu wani yaron da ke zuwa makaranta sama da shekaru biyu. Wannan bai dace ba.

A halin da ake ciki dai al'umomin yankin arewa maso yamma da kuma kudu na cikin wani yanayi na rashin tabbas a yankin na Kamaru da ke magana da harshen Ingilishi, bayan dakatar da harkoki da mayakan tawayen suka yi.