1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana fita a Saliyo saboda Ebola

Muntaqa AhiwaMarch 22, 2015

Tun farko dai gwamnati ta sanar da kafa dokar hana fitan a arewacin kasar da kuma babban birninta wato Freetown.

https://p.dw.com/p/1EvCT
Sierra Leone Ebola
Hoto: REUTERS/Baz Ratner

Shugaba Ernest Koroma na kasar Saliyo, ya bukaci hadin kan 'yan kasar sa ga kokarin da gwamnati ke yi na hana yaduwar cutar nan ta Ebola a kasar, biyo bayan dokar hana fita da ya sanar na tsawon kwanaki uku a kasar a ranar Asabar.

Tun farko dai gwamnatin ta sanar da kafa dokar ce a arewacin ta, da ma Freetown babban birnin kasar, inda a ranar Asabar ta sa ke fadadata.

A ranakun da wannan dokar ke aiki gwamnatin ta jaddada cewar dukkanin wasu wuraren hada-hada a fadin kasar za su kasance a rufe.

Cutar Ebola dai ta yi kamari cikin watannin baya a kasashen Guinea da Saliyon da ma kasar Liberiya, ta kuma halaka dubban mutane, abin da ya sanya kasashen lasar takobin ganin bayanta, ranar 16 ga watan Afrilu mai zuwa.

Sai dai baya ga Saliyon, ita ma kasar Liberiya ta fuskanci tsaiko, sakamakon samun wata mata da aka yi a kasar da ta bayyana alamun cutar a Juma'ar da ta gabata.