Dimukuradiyya na cikin rikici a wasu sassa
September 15, 2022Brazil na daya daga cikin kasashe 12 da tsarin mulkin dimukuradiyyarsu ta cikin gida ya fara karkata zuwa ka tsarin mulkin kama-karya, a cewar bayanai da wata cibiyar bincike mai zaman kanta da ke Jami'ar Gothenburg da ake kira V-Dem ta wallafa. Sauran kasashe 11 sun hada da Poland da Nijar da Indonesiya da Botswana da Guatemala daTunisiya da Croatia, Jamhuriyar Czech, da Guyana, Mauritius da kuma Sloveniya.
Cbiyar ta kuma gano wasu kasashe 17 da suka yi rashin nasara a yaki da wannan matsala cikin shekaru goma da suka gabata, ciki har da Turkiyya da Philippines da Hungary. V-Dem dai daya ce kawai daga cikin cibiyoyi da ke bin diddigin dimokuradiyya a duniya.
Fernando Bazzarro, wani dan kasar Brazil mai bincike na cibiyoyin gwamnati a Jami'ar Harvard ya ce: "A cikin shekaru goma da suka gabata, sannu a hankali an yi wani tsari na raunana jam'iyyun siyasa a matsayin masu shirya dimokuradiyya. Jam'iyyu masu karfi na taimakawa dimokuradiyya aiki. Idan ba su ba, dimokuradiyya za ta kasance cikin rauni saboda shugabanni masu son kan su. Idan aka zabi wadannan shugabanni a mukamai suna iya amfani da ofisoshinsu wajen yi wa dimokuradiyya rauni."
Chaina ba ta gudanar da zaben jam'iyyu barkatai
Duk da cewar ana iya alfahari da yadda kasasahe da dama suka fara tsarin dimukuradiyya fiye da shekaru 100 da suka gabata, an samu wannan salo na mulki ya fara samun tafiyar hawainiya ne a farkon shekarun 2000. Zurfafa nazarin bayanan yana nuna abin da ke faruwa a zahiri, wanda kan iya bada hasashen kasashen da dimokuradiyyarsu ke cikin rikici.
Masu bincike na V-Dem sun kasa kasashe zuwa rukuni hudu. A cikin tsarin mulkin kama karya da ke rufe kamar a Chaina da Qatar, ba a gudanar da zabukan jam'iyyu da yawa na shugaban zartarwa ko na majalisa. A kasashe masu cin gashin kansu kamar Turkiyya da Venezuela kuwa, ana gudanar da zabuka, amma ba cikin gaskiya da adalci ba.
A cikin tsarin dimokuradiyyar zabe irin su Brazil da Afirka ta Kudu, ana gudanar da zabuka cikin gaskiya da adalci, amma akwai rashin daidaito da kuma mutunta 'yancin wasu tsiraru. A cikin dimokuradiyya masu sassaucin ra'ayi, irin Jamus da Sweden, ana gudanar da zabe mai nagarta, da tabbatar da hakkokin tsiraru, da tantance aiki da daidaito tsakanin masu iko.
Ba mai tabo Vatican a fannin dimokuradiyya
Wannan rarrabuwar ka iya boye wasu muhimman ababai, in ji Bastian Herre, wani mai bincike a wata kungiya mai zaman kanta " Our World in Data" wanda ya yi bincike kan alakar da ke tsakanin akidun gwamnati da dimokuradiyya yayin da yake aiki wajen neman digirinsa na uku a fannin kimiyyar siyasa a Jami'ar Chicago.
Ya ce: "Da wannan, zamu iya sanin cewar Koriya ta Arewa da Iran ba dimokuradiyya ba ne yayin da Chile da Norway suke tsarin dimokuradiyya. Amma ba mu san matsayin karfin dimokuradiyyar Iran fiye da Koriya ta Arewa ba, haka kuma ba mu san yadda Chile ta gaza dimokradiyya fiye da Norway ba."
Kasashe 179 da V-Dem ta ware, kusan an raba su tsakanin masu gudanar da zabe ko rufa-rufa da dimokuradiyya masu sassaucin ra'ayi ko na zabe. Wasu kasashe da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da su, kamar Vatican ko San Marino, ba su da bayanai.