1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Diffa sun shiga tasku kan rikicin Boko Haram

Mahaman Kanta
February 20, 2019

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin farar hula masu rajin kare hakin bani adama sun koka kan yadda talakawa a jihar Diffa suka shiga cikin tsaka mai wuya kan rikicin Boko Haram.

https://p.dw.com/p/3Dkho
Nigeria Soldaten in Diffa
Hoto: Reuters/J. Penney

Kungiyoyin sun baiyana takaici cewa bayan halin kunci da 'yan Boko Haram da ke kai hare-hare da kashe jama'a suka jefa al’ummar Diffa a ciki, a hannu daya kuma jami’an tsaro da ke fafatawa da 'yan ta'addar, suna kame wasu mutanen da basu san hawa balantana sauka ba, ba tare da yin cikakken bincike ba.

Moussa Tchangari, shugaban hadaddiyar kungiyar dake kare hakin bani adama a Nijar, wato Alternative Espace Citoyen, ya bada misali da wani harin na baya-bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a kauyen Chetilari, dake jahar Diffa. Bayan barnar da 'yan ta'addar suka yi jami‘an tsaro sun kame wasu mutane takwas da suke zargi da 'yan Boko Haram ne.

Kungiyar ta ce ta gana da iyalan mutanen da aka kama da hakimin garin wadanda suka tabbatar musu cewa mutanen basu da alakar komai da 'yan Boko Haram,hasalima ba'a same su da wani makami ba.

Mousa Tchangarin ya kara da cewa tun lokacin da wannin fitinar ta taso a jihar Diffa, an kame kusan mutum 1500.

A nasa bangaren dan majalisa Hama Assa, shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokoki ya ce a matsayinsu na wakillan jama'a duk abinda bai dace da doka ba akwai matsala a ciki. Yace ya kamata su kiyaye kada su wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu.