1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deby ya murkushe juyin mulki a Chadi

May 2, 2013

Gwamnatin Chadi ta cafke wasu sojoji da kuma 'yan adawa bisa zargin yunkurin juyin mulki, tare da mikasu ga kotu domin fuskantar hukunci. Juyin mulki ba sabon abu ba ne a kasar.

https://p.dw.com/p/18QMF
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Chadi ta bayyana cewar ta yi nasarar murkushe wata manakisar da aka kitsa da nufin hambarar da shugaba Idriss Deby Itno daga kujerar mulki. Ministan watsa labaran kasar Hassan Sylla ben Bakari ne ya bayar da wannan sanarwa a kafar telebijin mallakar gwamnati, a inda ya ce tuni aka mika wadanda suka yi yunkurin juyin mulki ga kotun domin fuskantar hukunci. Har yanzu yanzu dai, ba a bayyana sunayen wadanda suka yi wannan yunkuri ba.

Rrundunar 'yan sandan Chadi ta nunar da cewa an cafke mutane da dama ciki har da sojoji da kuma dan majalisa Saleh Makki da aka zaba karkashin lemar adawa. Ita dai Chadi ta yi kaurin suna a fiskar tawaye da kuma juyin mulki. Ko da shi ma dai shugaba Deby da ke ci a yanzu, ta wannan kafa ya dare kan kujerar mulki a shekarar 1990. Tun a makon da ya gabata ne Idriss Deby Itano ya zargi gwamnatin makwanbiyar kasa Libya da marawa 'yan tawaye baya domin hadasa rikicin a kasar da ya ke shugabanta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu