Dbeibah da Bachagha: Wa ke mulkar LIbiya?
March 1, 2022Talla
'Yan majalisa 92 ne suka kada kuri'ar amincewa da gwamnatin Fathi Bashagha daga cikin 101 da suka halarcin zaman a birnin Tobruk da ke gabashin kasar. Sai dai wannan matakin zai iya sake jefa Libiya cikin rikicin shugabancin tsakanin bangarori da ke gaba da juna, kamar yadda ta kasance tsakanin a shekarun baya.
Idan za a iya tunawa, a ranar 10 ga Fabrairu ne, majalisar ta Libiya ta nada Bachagha domin ya maye gurbin Dbeibah a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi. Sai dai firaminista da ke ci ya ce ba zai mika mulki ba matakiar da zababbiyar gwamnati ba ce. Ire-iren wadannan rigingimun siyasa sun sa a dage zabe sau biyu a Libiya, duk da fatan da kasashen duniya ke yi na kawo karshen rudanin da ya addabi kasar.