DAX Kasuwar hannayen jari ta Frankfurt
August 12, 2008Masu sauraro asalamu alaikum barka mu da warhaka lale marhabin da sake saduwa daku a wani saban shiri na ciniki da masana´antu.
A wannan karo shirin zai koma da mu zuwa birnin Fankfurt na nan ƙasar Jamus, inda za mu yada zango a kasuwar hada hadar hannayen jari ta wannan birni wato Dax ɗaya daga mafi girma a duniya.
Za mu ji yadda masu saye da sayarwa ke gudanar da hada hada hannayen jarin.
Wakilin DW ne Matt Herman yayi tattaki har zuwa wannan kasuwa domin shirya tsarabar, da ni YSM zani fasara maku.
Kasuwar hada -hadar hananyen jari ta birnin Frankfort, da ak fi sani da suna Dax kokuma Deutscher Aktien Index a halshen jamusanci,na daya daga kasuwannin hannayen jari da suka fi girma a duniya.
Manyan kamfanonin Jamus, kamar su Siemens, Wolkswagen, Daimler Chrysler, Allianz Ag, Deutsche Telekom, Bayer Ag da dai sauran su, suka haɗu domin girka wannan cibiya.
An ƙaddamar da wannan kasuwa, tun 2 ga watan Janairu na shekara ta 1989, wannan kasuwa na matsayin ma´aunin dake nuna cigaba, ko kuma koma bayan tattalin arzikin ƙasar Jamus.
Olivier Roth, na ɗaya daga dullalan dake hada -hada a cikin wannan kasuwa ya kuma bayyana yadda suke gudanarwa da harakoki:
"Aikinmu a cikin wannan kasuwa shine na sada hulɗoɗi tsakanin masu saye da masu sayar da hannayen jari.
Kuma a duk lokacin da aka saida hannu jari ɗaya, muna da kamashon da ake biyan mu, ɗaya kenan , na biyu,muna daidaita sahun yadda tsarin kasuwar ke tafiya.
Misali muna da masaya dubu huɗu, wanda ke bukatar sayen hannun jari na Euro huɗu, sannan a lokaci guda muna da masu sayarwa dari hudu, wanda ke bukatar saida hannayen jari na euro huɗu.
Nauyi ya rataya akanmu, mu daidata wannan kasuwa ta yadda kowa zai samu riba.
Wannan na nufi idan muna da masu sayarwa mutane dubu hudu ,da masu saye dubu ukku, sai mu saida giɓin da aka samu, wato hannayen jarin mutane dubu ɗaya kenan ga kampafanoni.
To saidai a nan akan iya cin riba ko kuma a faɗi."
Ko wace cibiyar hannayen jari ta ƙunshi kamfanoni da dama, da suka haɗa ƙarfi, domin tafiyar da harakoki.
A wannan lokaci da yanar gizo da kuma na´ura mai ƙwaƙƙwalawa suka zama ruwan dare gama duniya, ana gudanar da harakokinta wannan hanya.
Daga nan zaune masu saye da masu sayarawa suna da cikaken labari a game da halin da akasuwa ke ciki ako ina cikin duniya , saboda haka suna la´akari da da bayyanan da ke zo masu daga na´ura mai ƙwaƙƙwalwa saboda haka mafi yawan lokatta sukan zura ido ga na´urar domin binciken bayyanan dake faɗowa.
........................Atmo..........................
Mafi yawan masu tafiyar da wanan hada hada kamar shikansa Roth, ba su sayen hannu jari ba tare da suna da tabbas ba na samun riba.
" Muna da yaunin tafiyar da kamfanoninmu. Saboda haka dole muyi takatsantsan wajen sayen hannayen jari, don riga kafi ga abkuwar asara, domin idan muka yi kuskure, za mu tafka asara mai yawa.
saboda haka, mafi yawan mutanen dake gudanar da wannan hada hada na da albashi mai tsoka, sannan dattijawa ne masu shekaru 60 zuwa 65 ,wanda suka ƙure a cikin aikin".
Shima Guido Prey, ya jimma ana damawa da shi a kasuwar hannayen jari, ya ce a duk tsawan lokacin da yayi bai taɓa ganin faɗuwa da saukar ciniki cikin ƙiftawa da bissimillah, kamar irin halin da ake ciki, inda yanzunan nan farashe ya tashi kuma yanzunan ya sauka.
To saidai ya yaba da cigaban da aka samu, ta fannin sadarwa, wanda ya sauƙaƙa gudanar da harakokin kasuwar.
"Yau shekaru 40 kenan ina wannan kasuwanci, na san ƙabli da ba´adinsa baki ɗaya, da farko an sha fuskantar matsaloli, har zuwa lokacin da aka fara samun na´ura sallula, amma a yanzu, mun shiga wani saban zamani, inda komai ya cenza tare da na´ura mai ƙwaƙƙwalwa, da amfani da yanar gizo, yanzu tsofan yayi ya kau."
Saidai a halin da ake ciki, hada hadar hannayen jari a dukan manyan kasuwanin duniya ta shiga wani yanayi na rashin tabass, a saboda haka, ya zama wajibi kamfanoni masu saye kokuma saida hannayen jari ,su ƙarfafa nazari ,inji Guido Prey ,domin muddun babu matakan sa ido, ba da ɓata lokaci ba, za a fuskanci asara mai tarin yawa.
" A cikin´yan kwanakin nan , kasuwar ta gurɓace, har kullum farashe sai ƙara faɗuwa yake.
Saboda haka, cilas mutum yayi tunani kafin ya sayi hannun jari, mussamman wanda ya shiga halin wantare".
Hada hadar hannayen jari ,kasuwa ce mai cike da haɗari , to amma kuma ta na ɗaya daga kasuwancin da, a cikin ɗan lokaci ƙalilan mutum ke tara dukiya, a game da haka, Guido ya bayyana shawar wannan sana´a.
"Ya kamata mutum ya ƙaunacin sana´ar shi,ko da wace iri ce, muddun ya na buƙatar samun ci gaba a cikin ta.
Duk da cewar ba za taɓa samun gamsuwa ba 100 bisa 100,to amma abu mai mahimmanci shine nuna shawa a gare ta.
Mutum ya san da cewar ba kowa ke iya ko wace sana´a ba.
Ni dai kam sana´ar hada hadar hannayen jari ta karɓe ni,amma idan mutum ya ji ba zashi iya sana´ar da yake ba, sai ya cenza wata sabuwar sana´a da tafi dacewa da shi."
Ƙila ya cenza da aikin jarida!!!.