Dawo da koyar da tarihi a manhajar karatu a Najeriya
November 29, 2022Tun shekaru 13 da suka gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta soke tsarin koyar da tarihi a makarantun sakandaren kasar inda aka maye shida wani darasin daban. To sai da masana tarihi da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin koyar da ilimin tarihi sun yi ta fadi tashin ganin an dawo shi saboda muhimmancin sa musamman ga yara da ke tasowa ganin su ne manyan gobe.
A wannan lokacin ne gwamnatin Najeriyar ta mayar da tsarin koyar da darasin a manhajar koyarwa na makarantun Najeriya abin da ya haifar da ra'ayoyi musamman daga malamai a wannan fanni na ilimi. Yawancin malaman da ke koyar da tarihin sun bayyana farin ciki da wannan mataki na gwamnati inda suka ce darasin na da muhimmanci kwarai.
Su ma masana da masharhanta sun ce yana da kyau dalibai su san asalinsu da kuma tarihin abubuwa da suka shafi rayuwarsu da ta sauran al'amuran duniya, abin da ya suka ce gwamnatin ta yi tunani mai kyau. Su ma iyayen yara sun nuna jin dadi da sake dawo da tsarin koyar da tarihin a makarantun sakandaren na Najeriya saboda muhimmancin hakan ga makomar yara masu tasowa.
Yanzu haka dai gwamnatin Najeriyar ta shirya samar da malamai sama da dubu uku da za a sake ba su horo ta yadda za su ci gaba da koyar da tarihi a makarantun na ganba firamare wato aakandare a fadin kasar.