Shirin na wannan mako ya yi nazari kan matsalar rashin aikin yi da ke janyo gurbacewar dabi'un matasan jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar. Jihar ta Diffa dai na daga cikin yankuna da ke fama da matsalar tsaro, sai dai Jamus na bayar da tallafin domin shawo kan matsalar.