1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan kasuwa mai tallafawa jama'a

June 21, 2017

Wani matashi dan kasuwa a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya sadaukar da kansa wajen tallafa wa al'ummar kauyensu inda ya samar da abubuwa daban-daban ciki kuwa har da gina makaranta da kuma daukar malamai aiki.

https://p.dw.com/p/2f62H
Mosambik Schule in Majune
Ginin makaranta ta Islamiyya na daya daga cikin tallafin da Alhaji Ibrahim Teacher ya bayar a kauyensu na Kaura da ke KatsinaHoto: DW/M. David

Tallafi ta fuskar samar da ilimi na addini da gyaran hanya da ginin masallaci dai na daga cikin irin abubuwan da matashin mai suna Alhaji Ibrahim Teacher ke yi a kauyensu na Kaura da ke jihar Katsina wadda ke arewa maso yammacin Najeriya. Matashin ya ce ya dau gabarar tallafawa mutanen saboda a cewarsa ''mutanen 'yan uwana ne kuma akwai yiwuwar watara mu koma kauyen''.

Wadannan aiyyuka dai sun lakume miliyoyin nairori, lamarin da ya sanya al'ummar wannan kauye na Kaura yin Allah san barka da wannan tallafi da wannan taliki ya ke yi musu inda mutane irinsu Bello Kaura da Abdullahi Garba da Nura Salele suka yi masa addu'ar samun karin cigaba a harkokinsa na yau da kullum a lokacin da suka yi hira da wakilin DW da ke Katsina Yusuf ibrahim Jargaba.