1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Saif al-Islam Gaddafi zai tsaya takara

Abdoulaye Mamane Amadou
November 14, 2021

A shirye-shiryen zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisun dokokin watan gobe a kasar Libiya, Saif al-Islam Gaddafi zai yo takarar shugaban kasa

https://p.dw.com/p/42yi9
Libyen Sebha | Saif al-Islam al-Gaddafi registriert sich als Präsidenstchaftskandidat
Hoto: Khaled Al-Zaidy/REUTERS

Dan tsohon shugaban kasar Libiya marigayi Muammar al-Gaddafi, Saif al-Islam Kaddafi ya kaddamar da takardarsa na tsayawa takara a zaben shuagban kasar da ake shirin gudanarwa a cikin watan Disamba.

Tuni ma dai hukumar zaben kasar ta Libiya ta bakin mataimakin shugabanta Abdel Hakim al-Chaab ta tabbatar da wannan labarin a yayin da yake zantawa da wata kafar talabijin mallakar kasar a birnin Sabha da kudanci.

Ita dai kasar ta Libiya ta fada ne yakin basasa, tun bayan da kisan tsohon shugaban kasar Muammar al-Gaddafi shekaru da dama da suka wuce, lamarin da yakai ta ga darewa gida biyu, tare da zama mashigi na miyagun makamai da safarar bakin haure tsakaninta da kasashen Afirka na kudu da hamadar sahara