1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazoum ya gana da likitansa

Suleiman Babayo AH
August 12, 2023

Ana ci gaba da neman hanyoyin diflomasiyya na warware rikicin siyasar Jamhuriyar Nijar yayin da hambararren Shugaba Mohamed Bazoum ya gana da likitansa.

https://p.dw.com/p/4V6Gd
Bazoum a birnin Paris na Faransa
Hambararren Shugaba Mohamed Bazoum na Jamhuriyar NijarHoto: Stevens Tomas/ABACA/IMAGO

Rahotannin daga birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar na cewa hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ya gana da likitansa yayin da sojojin da suka kifar da gwamnatinsa suke ci gaba da tsare shi. Ranar 26 ga watan jiya na Yuli sojoji suka kifar da Bazoum mai shekaru 63 da haihuwa daga madafun ikon kasar.

Haka na zuwa lokacin Kungiyar ECOWAS ta sanar da dage taron manyan hafsoshin sojin kasashen yammacin Afrika da aka shirya gudanar da shi a babban birnin Accra na kasar Ghana bisa tattaunawa bayan da kungiyar ta shirya da rundunar ko-ta-kwana bisa batun na Jamhuriyar Nijar.

A wani labari wata tawogar shugabannin addini daga Najeriya ta isa birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar, domin tattaunawa da sojojin da suka kwace madafun ikon, kamar yadda wata majiya ta kusa da sojojin ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Sabon Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine da sojojin suka nada ya tarbi tawogar, yayin da shugabannin kasashen na Afirka ta Yamma karkashin kungiyar ECOWAS suka ce za su ci gaba da neman hanyoyin diflomasiyya wajen magance rikicin siyasar.