Daliban Nijar na ci gaba da bore
September 13, 2017Daliban sun soma boren bayan wani yajin kin komawa karatu a farkon wannan watan suna mai cewar sai gwamnati ta shafe musu hawaye ta hanyar biyan su kudaden alawus alawus da suka zarta na watanni biyu, tarin daliban jami'ar Abdou Moumouni Dioffo sun yi tir da Allah-wadai da halayyar da gwamnati ke nunawa fannin na ilimi mai zurfi musamman ga manyan jami'o'in kasar. Wasu daga cikin dalilan da suka haifar da boren daliban na wannan lokacin sun hada da rashin ingantaciyar rayuwa a jami'a da kulawa da halin da dalibai suke ciki musamman ma wuraren kwanciya da abinci baya ga wuraren daukar karatu da kuma uwa uba kudaden alawus.Malam Tsalha Kaila mataimakin sakataren zartarwa na kungiyar daliban jami'ar Yamai UENUN ya ce abinda takaici ‘‘Ya ce mun lura da ana mana zagon kasa dalilin da ya sa muka ce gara mu fito mu nuna rashin jin dadinmu game da abubuwan da ke wakana saboda yadda shuwagabannin su ke ta tabarbarar da harkokin jami'ar nan idan kuka duba a yanzu daliban nan da yawa ne ke cikin wani mawuyacin hali wasu ba wurin kwanciya hakan kuma yanzu hakan wasu ba su da wuraren daukar karatu an shafe tsawon shekaru anan cewar za a gina wuraren kamar ana gina Nijar‘‘
Matsalar ta haifar da halin tagayyara ga daliban na jami'ar birnin Yamai akalla dubu 25 baya ga rashin tsari da rashin ingancin karatu da ake samu daga malaman jami'ar abinda ya haifar da tabarbarewar karatu, daliban dai sun kafa manyan shingaye domin tattare duk wasu hanyoyin da ke kai ga zuwa jami'ar a wani mataki na kawar da duk wata dama ta hana jami'an tsaro shiga da zummar kaucewa abubuwan da suka faru a ranar 10 ga watan Afrilun da ya gabata inda ka samu asarar rai na wani dalibi.Wannan shi ne bore na biyu a kasa da mako guda da daliban jami'ar suka gudanar suna masu bukatar kawo musu agaji don inganta rayuwarsu ta fannin ilimi.