1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar Bouteflika na fuskantar cikas

Abdul-raheem Hassan
March 3, 2019

Daruruwan dalibai sun fantsama kan titunan Algiers babban birnin kasar Aljeriya domin yin zanga-zangar nuna adawa da matakin Shugaba Abdelaziz Boutaflika na nuna sha'awar takarar shugabanci karo na biyar.

https://p.dw.com/p/3EO2y
Algerien - Studentenproteste
Hoto: picture-alliance/F. Batiche

A cikin fushi daliban dauke da kwalayen rubutu a kantituna su na shewar cewa "Ba mu yadda ba, muna bukatar canji." An tsaurara matakan tsaro a muhimman wurare da ke cikin birnin, yayin da motocin tsaro ke ta sintiri a sassa daban daban domin taka wa masu bore birki wajen hana Shugaba Boutaflika mika takardun takararsa karo na biyar a hukumance.

Shugaba Abdelaziz Boutaflika yana da shekaru 82, ya yi mulkin shekaru 20 amma tun shekarar 2013 rashin lafiyar shanyewar barin jiki ya hanashi fitowa cikin jama'a, abinda wasu 'yan kasar ke ganin ba shi da lafiyar iya shugabanci amma shugaban ya ce a shirye ya ke ya sake wani wa'adin mulki.