1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakon sakamakon zabe a Gabon

August 29, 2016

Dan takarar jam'iyyar adawa a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Gabon Jean Ping ya ayyana samun nasara, batun da bangaren gwamnati suka bayyana da mai hadari ga zaman lafiyar kasar.

https://p.dw.com/p/1JrT3
Al'ummar kasar Gabon na dakon sakamakon zaben shugaban kasa
Al'ummar kasar Gabon na dakon sakamakon zaben shugaban kasaHoto: Reuters/E. W. Obangome

Bangaren shugaban kasa mai ci Ali Bongo wanda shi ma ya tsaya takarar shugabancin kasar da nufin yin tazarce dai, sun ce ayyana samun nasar ba tare da kammala kidayar kuri'u domin samun cikakken sakamako ba, babban kuskure ne. Bongo mai shekaru 57 a duniya, na mulkin kasar ta Gabon tun daga shekara ta 2009 bayan da mahaifinsa Omar Bongo wanda ya kwashe tsahon shekaru 41 yana mulkin kasar ya rasu. A nasa bangaren Jean Ping da ke da shekaru 73 a duniya, shima ya kwashe tsahon shekaru yana rike da mukami a gawamnatin Omar Bongo. Al'ummar kasar dai na cikin fargabar sake barkewar rikici makamancin wanda ya afku a shekara ta 2009 bayan da aka ayyana Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.