Dakarun Ouattara na samun galaba a faɗan da suke yi da na Gbagbo a birnin Abidjan
April 1, 2011A ƙasar Cote d'Ivoire ana ci-gaba da ɓarin wuta na manyan makaman yaƙi a kusa da fadar shugaban ƙasa Laurent Gbagbo ke da zama. Wata majiyar soji ta kusa da Gbagbo ta ce dakarun dake biyayya ga Alassane Ouattara mutumin da duniya ta yi na'am shi ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, sun kai farmaki akan fadar shugaban ƙasa dake birnin Abidjan, amma sojojin Gbagbo sun mayar da martani.
Tun a cikin daren wannan Alhamis aka yi ta jin ƙaran harbe harbe na manyan makaman yaƙi daga unguwar Treichville dake kusa da wani sansanin da sojojin Laurent Gbagbo ke amfani da shi don kare wata gada da ta doshi tsakiyar birnin Abidjan. Sannan da tsakan dare aka fara fafatawa tsakanin sojojin dake biyayya da shugaban mai barin gado da sojojin Alassane Ouattara a kusa da harabar fadar Gbagbo.
Ko da yake da wuya a san inda Gbagbo ɗin ya ke a yanzu amma an rawaito jakadan Faransa a Cote d'Ivoire Jean-Marc Simon na cewa shugaban mai taurin kunne ya maƙale a cikin fadar ta sa, bayan da ya tsere daga gidansa dake wata unguwar ta birnin Abidjan. To sai dai kawo yanzu ba za a iya tabbatar da kalaman jakadan ba cewa 'yan tawaye sun ƙwace gidan Gbagbo da kuma fadarsa domin duk ƙoƙarin da aka yi na tuntuɓar na hannun damar Gbagbo ya ci-tura.
Ana ƙara mayar da Gbagbo saniyar ware
Tun bayan sanya masa ƙarin takunmin da kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi, ruwa ya fara ƙarewa Gbagbo, inda a cikin makon manyan sojojin sa suka fara juya masa baya. Kuma sojojin Ouattara ke ci-gaba da ƙwace wurare masu muhimmanci a ƙasar. Alassane Ouattara wanda ƙasashen duniya suka yi amanna shi ne halattaccen shugaban ƙasar biyo bayan zaɓen ƙarshen shekarar bara ya yi kira ga sauran hafsoshin sojin ƙasar da har yanzu ke marawa Gabgbo baya da su canza sheƙa.
"Ina kira gare ku dukka, ko Janar janar ne ko kuratan soji ne da ma sauran jami'an soji a duk inda kuke a cikin ƙasar, da ku miƙa kanku domin kare ƙasarku."
Wata majiyar soji da ba ta so a bayyana sunanta ba ta ce 'yan Jandarma da sojoji kimanin dubu hamsin sun bar barikokinsu. Sai mayaƙa da ɗalibai magoya bayan Gbagbo kaɗai da yawansu bai wuce dubu biyu ne suke ci-gaba da faɗan kare gidansa. Gilles Yabi na ƙungiyar ƙasa da ƙasa dake bin diddiginn rikikce rikice a duniya ya ce yanzu haka an shiga matakin ƙarshe na yin kare jini biri jini a birnin Abidjan.
"Yanzu haka dai dakarun Ouattara sun na cikin Abidajn kuma ba su gamu da wata turjiya mai ƙarfi ba. Amma dole a jira a ga irin dubarun da za su bi bayan sun ƙwace birnin. Shin za su fatattaki Gbgbo daga fadar gwamantin da ƙarfin hatsi ko kuma za su ba shi wasu kwanaki domin ya tattara na ya na sa ya fice ba tare da an zubar da jinin bayin Allah a wannan birni mai miliyoyin mazauna ba?"
A halin da ake ciki ƙungiyar tarayyar Afirka AU ta yi kira ga Gbagbo da yawa Allah da Annabinsa ya sauka ya ba wa Ouattara. Sannan Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna damuwarta ga rahotannin dake cewa dakarun Ouattara na aikata ta'asa akan mutane.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar