Dakarun Libiya da na Haftar na bata kashi
April 29, 2019Talla
Sojojin da ke biyeyya ga madugun yakin Libiya Khalifa Haftar da masu goyon bayan gwamnatin Tiripoli sun yi wani gumurzu a wannan Litinin, a kusa da wasu rijiyoyin man fetur na Al-Sharara mafi girma da ke kudancin kasar. Rijiyoyin na samar da danyen man fetur akalla ganga dubu 315 a kowace rana daga cikin gangar danyen mai fiye da miliyan daya da kasar ta Libiya ke samarwa a rana.
Sai dai a lokacin da yake magana da manema labarai, kamfanin ya ce gumurzun da dakarun bangaroron biyu suka yi bai shafi ko guda daga cikin ma'aikatansa ba. Ya zuwa yanzu bata kashin da bangarorin ke yi a kasar sun halaka mutane 278 akalla tare da jikkata wasu fiye da dubu daya kana kuma akalla dubu 40 suka kaurace wa gidajensu in ji Hukumar Lafiya ta Duniya OMS.