Dakarun Isra'ila sun janye daga Jenin
July 5, 2023Sojojin sun yi ikirarin cewa sun yi barna sosai a kan kungiyoyin 'yan ta'adda a sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Jenin, a hare-hare ta sama da kuma farmakin sojoji ta kasa. Gabanin janyewar dai, Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin sake kai makanmancin wannan harin idan bukatar hakan ta taso.
Tun a farkon shekarar 2022 ne, Isra'ila ke kai jerin hare-hare yankunan Falasdinawa a wani mataki da ta ce ramuwa ce ga munanan hare-haren Falasdinawan. Rahotanni sun yi nuni da cewa, mayakan Hamas sun harba wasu rokoki zuwa Isra'ila, inda ita ma Isra'ilar ta kaddamar da wasu hare-hare ta sama a wannan Larabar.
Hukumomin kiwon lafiyan Falasdinu sun ce kimanin Falasdinawa 13 ne aka kashe tun fara farmakin, sai dai dakarun Isra'ila sun yi ikrarin halaka 'yan ta'adda ne kawai.