Huldar Italiya da Faransa na nan ba sauyi
January 22, 2019Talla
Dangantaka tsakanin Italiya da Faransa na nan yadda aka santa a matsayin kawayen juna duk kuwa da takaddama da ke wakana tsakanin kasashen biyu kan batun 'yan gudun hijira. Firaministan Italiya Giuseppe Conte ya bayyana haka a wannan Talata a kokari na yayyafa ruwan sanyi a musayar zafafan kalamai da ake yi tsakanin mahukuntan na biranen Rome da Paris.
A ranar Litinin ce dai Faransa ta nemi jakadanta a kasar ta Italiya ya koma gida bayan da mataimakin firamanistan kasar ta Italiya Luigi Di Maio ya zargi mahukuntan Paris da haifar da yanayi na talauci a kasashen Afirka. Abokin aikinsa ma Matteo Salvini ya bi sahunsa inda ya zargi Faransa da rashin tabuka komai wajen maido da zaman lafiya a kasar Libiya.