Dabi'ar sace-sacen mutane na kara kamari a Najeriya
March 19, 2024Mutane kusan 500 ne aka sace bayan kashe da daman gaske a wani abin da ke kara fito da irin girman matsalar rashin tsaron da ke aadbar makarantun tarayyar Najeriya. Duk da cewar shekarar 2024 na kan gaba wajen samar da kudi domin kalubalantar annobar rashin tsaro, amma kasar na hangen ta'azzarar rashin tsaron a ko'ina. Abdul Aziz Sulaiman da ke zaman kakakin kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta Northern elders, ya ce babu gaskiya a bangaren 'yan mulkin bisa batun tsare rayukan al'ummar Arewa.
Kokarin sauke bashi ko neman mafitar rashin tsaro?
Naira Triliyan uku ne ko kuma kaso 13% na daukacin kasafin kudin bana ne aka ware dominkokarin magance rashin tsaro da ke zama annoba ta kan gaba cikin Najeriya. Ko bayan mika daukacin mukamai na tsaron bisa shugabannin da cibiyarsu ke a Arewa, amma an kare a ta'azzarar annobar satar 'yan kasa a Kaduna da mafi yawan sassa na Arewa. Dr Yahuza Getso da ke sharhi kan rashin tsaron ya ce karuwar sace 'yan kasar don neman kudin fansa na zaman alamun zafi a bangaren barayin da ke kara fuskantar hari na jami'an tsaro.
Ana wasan buya tsakanin jami'an tsaro da barayin daji
Akalla jihohi 19 na tarayyar Najeriya ne ya zuwa yanzu ke fama dafargabar tsaro musamman annobar sace mutane a cikin kasar da kuma ke kallon rikicin cin hanci a matakan mulki da dama. Arewacin tarrayar Najeriyar na shirin kallon karin rikici baya ga batun karuwar talauci, a cewar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan batun harkokin mulki na tarayyar Najeriya.