1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola tana kara yaduwa

June 24, 2014

Annobar cutar Ebola tana yaduwa cikin wasu kasashen na yankin yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/1CP13
s
Hoto: CELLOU BINANI/AFP/Getty Images

Kungiyar likotoci ta na gari na kowa, ta ce annobar Ebola na bazuwar da ke alamun tana fin karfin a yi mata linzami. A yanzu da aka kwantar da kimanin mutane 60 da suka kamu da cutar, kungiyar ta ce idan aka yi la'akari da sarkiyar kan iyakokin da kuma yadda cutar ta bazu ya nuna akwai babbar barazana. A yanzu haka cutar na bazu da kashi 90 cikin dari.

Cutar Ebola da ta bulla a kasar Gini Konakry kafin ta bazu zuwa Saliyo da Laberiya, inda ta hallaka kimkanin mutane 340 a kasashe ukun, kamar yadda alkaluman Hukumar Lafiya ta duniya suka nunar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo