1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Ebola ta zama barazana

September 12, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yaduwar cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/1DBag
Hoto: DW/J. Kanubah

Majalisar Dinkin Duniya ta ce barkewar cutar Ebola a wasu kasashen yankin yammacin Afirka ta zama bala'i mafi muni na cutar inda ta hallaka fiye da mutane 2,400. Shugabar Hukumar Lafiya ta Duniya Margaret Chan ta yi gargadin cewa rashin daukan matakan da suka dace daga kasashen duniya, ka iya kara rikirkita lamura.

Shugabar ta ce kasashen uku na Gini, da Laberiya da kuma Saliyo suka fi tagayyara sakamakon barkewar cutar.

Kasar Cuba ta yi alkawarin tura tawogar lafiya mafi girma zuwa kasashen Afirka da aka samu barkewar cutar Ebola, domin ba da gudumawar dakile cutar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba