Cutar Ebola ta sake bulla a babban birnin kasar Saliyo
June 24, 2015Talla
Gwamnatin kasar Saliyo da ke yankin yammacin Afirka ta bayyana sake samun sabbin kamuwa a cutar Ebola, a birnin Freetown fadar gwamnatin kasar mai dauke da mutane milyan daya da dubu-dari-biyu, abin da ya kawo karshen fata kan dakile cutar a wannan birni.
Hukumar kula da cutar Ebola ta kasa ta ce an samu mutane uku sabbin kamuwa da cutar cikin wata unguwa ta marasa galihu, makonni uku aka shafe ba tare da samun wanda ya kamu da cutar ba. Tuni jami'an kiwon lafiya suka fara kula da mutane shida bisa yuwuwar bayyanar cutar ta Ebola.
Barkewar cutar ta Ebola ta hallaka fiye da mutane 11,000 galibi a kasashen Laberiya, da Saliyo, da kuma Guinea.