Cutar Ebola na ci gaba da yaduwa a Afirka ta Yamma
May 28, 2014Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ce Conakry babban birnin kasar Guinea ya sake samun wani da ya kamu da cutar Ebola a cikin wata guda yayin da wuraren da suka fuskanci barkewar annobar a da suka ba da rahoton sabbin kamuwa da ita a makon da ya gabata. Sake bullar cutar cikin kasa da watanni biyu, wadda mahukunta a kasar Guinea suka ce sun shawo kanta, na barazana ga yakin da ake yi da kwayoyin cutar a yankin Afirka ta Yamma da ke fama da sukurkucewar tsarin kiwon lafiya da kuma rashin cikakken tsaro a kan iyakokin kasashensa. A farkon wannan makon kasar Saliyo ta tabbatar da bullar cutar ta Ebola ta farko a cikin kasar, wadda kuma ta hallaka mutane biyar. Hukumar lafiya ta WHO ta ce cutar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 185 a kasar Guinea tun bayan bullarta cikin watan Maris. Sannan ta hallaka mutane 11 a Liberiya tun bayan bullarta a can ranar tara ga watan Afrilu.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar