CSU ta lashe zaben jihar Bavaria
September 16, 2013Sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a jihar Bavaria dake kudancin nan Jamus, ya nuna cewa jam'iyyar Christian Social Union, CSU, ita ce ta samu gagarumin rinjaye, yayin da jam'iyyar FDP, wadda ta kasance cikin gwamnatin hadaka da CSU ta rasa gurbi a majalisar jihar.
Ita dai jam'iyyar CSU ta na kawance ne da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kuma ta samu sama da kaso 48 na kuri'un da aka kada a yankin Bavaria, inda takwararta ta FDP da suka kasance cikin gwamnatin hadaka da ke jagorantar jihar tsahon shekaru 5, ta samu sama da kaso uku kacal, wanda ya gaza kaso biyar din da ake bukata domin samun wakilcin kujeru a majalisar dokokin jiha.
Angela Merkel dai na neman sake darewa kan kujerar shugabancin gwamnatin Jamus a karo na uku, a babban zaben da za a gudanar a ranar 22 ga wannan wata na Satumba da muke ciki.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal