Legas ta jinkirta bude masallatai da coci
June 16, 2020Dama dai gwamnatin ta so bude masallatan Jumma'a da coci a ranakun 19 da 21 ga wannan watan na yuni domin bayar da damar yin Ibada ga jama'a. Sai dai a wani jawabin da gwamnan jihar ta Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi a yammacin Talatar nan ya ce sun soke wannan yunkuri.
''Zamu jingine batun bude wuraren ibada har sai abin da hali yayi. Mun yi nazari mai zurfi a kan halin da muke ciki dangane da coronavirus kuma nazarinmu ya nuna mana cewa babu shakka mu dakatar da aniyarmu ta bude wuraren ibadar.'' inji Gwamnan jihar ta Legas.
Jihar ta Legas dai ita ce jihar da tafi kowace jiha a Najeriya yawan masu cutar corona. Alkaluma na baya-bayan nan da cibiyar yaki da yaduwar cututtuka ta kasar, NCDC, ta fitar sun nuna cewa Legas na da akalla mutum 7,300 wadanda suka kamu da wannan ciwo a cikin mutane kimanin 16,600 da suka kamu da ciwon a Najeriya baki daya.