COVID-19: An hana fita a fadin Indiya
March 22, 2020Talla
Indiya ta sanya dokar hana fita na yini guda, matakin da Firaminista Narendra Modi ya ce gwaji ne kan yadda kasar za ta iya yakar annobar da ta bulla yanzu a duniya.
Hotunan bidiyo a Indiya sun nuno yanda titunan biranen New Delhi babban birnin kasar da Mumbai da ma Kalkota suka yi wayam, inda kalilan ne daga muhimman shaguna ke harkoki, sai kuma ma'aikata na bukatar gaggawa.
Sama da mutum 300 ne suka kamu da cutar a Indiya mai mutum sama da biliyan guda, kasar da ake dari-dari da munin annobar COVID-19 muddin ta fara bazuwa cikin al'umar kasar.
Akwai ma wadanda ke damuwa kan yiwuwar alkaluman wadanda suka kamu ya zuwa yanzu a Indiyar, sun zarta adadin da hukumomi suka sanar. Matakin dai ya shafi dukkanin hanyoyi na zirga-zirga.