1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudaden da ake aikawa daga waje zuwa Afirka sun ragu

Daniel Pelz SB
May 26, 2020

A kowace shekara dubban milyoyin dala 'yan Afirka mazauna kasashen waje ke aikiwa zuwa nahiyar ga iyalai. Amma matsalar annobar coronavirus tana kawo cikas da sakamako mai muni a wannan bangaren. 

https://p.dw.com/p/3clR9
Western Union Geld Geldtransfer Sri Lanka
Hoto: AFP/Getty Images

Wannan matsala za ta haifar da raguwar kimanin kashi 23 cikin 100 na kudin da 'yan Afirka ke aikewa gida. Adadi mafi yawa a tarihin tura kudin tun lokacin da aka fara tattara alkaluman a shekarun 1980 kuma Dilip Ratha na Bankin Duniya ya yi karin haske bisa dalilan:

"Galibin masu hijira ba kwararru ba ne. Suna aiki a bangaren tattalin arziki da ba na gwamnati ba, kamar misali shaguna, otel, yawon bude ido, aikin gona. Wasu kuma aikinsu na lokaci zuwa lokaci ne. Wadannan masu hijiran yana da sauki su bace a lissafinsu ne na farko da za su iya rasa albashi da abun yi."

Iyalai a Afirka na cikin damuwa saboda rishin samun kudaden aike

Symbolbild Überweisungen nach Afrika
Hoto: picture-alliance/Godong

Ibrahima Bah daga kasar Guinea mazaunin birnin Paris na kasar Faransa yana cikin wdadanda suke fuskantar irin wannan kalubale yayin da matarsa da yara uku ke ci gaba da kiransa domin tura kudin da ya saba: "Iyalai suna ci gaba da kiranmu. Sai dai idan babu aiki ga dokar hana fita, lamarin ya zama mai sarkakiya. Iyalan a kanmu suka dogara." Baki da dama suna cikin irin wannan yanayi. Galibin kudin da suke turawa kan iya ciyar da iyali misali mai mutane hudu. Kudin da ake turawa nahiyar Afirka sun yi matukar karuwa a shekarun da suka gabata. Wani mai suna Djibo da ke Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar ya bayyana irin halin da suka shiga: ''Yar uwata wadda take rayuwa a Fransa tana neman turo wa mahaifiyarmu kudi. Ta ba da kudin ga wani wanda yake rayuwa a birnin Marseille na Faransa. Ya kira ya shaida mana mun je wajen dan-uwansa a gida da ke birnin Yamai na karba. Abin yana da sarkakiya sakamakaon cutar Covid-19."

Afirka ta fi kowace nahiya jin radadin rishin aika kudaden saboda corona

Destination Europe – Kapitel-Nr. 7
Hoto: LAIF

A duniya baki daya Indiya ce kasa ta farko da aka fi samun masu tura kudi gida, sai kasashen Chaina ta biyu da Mexiko ta uku. A jerin 10 na farkon Masar tana matsayi na biyar yayin da Najeriya take ta shida. Amma nahiyar Afirka ke kan gaba wajen dandana kudarta. A cewar Jacob Omolo masanin tattalin arziki na Jami'ar Kenyatta da ke Kenya irin wannan kudin na da tasiri ga Afirka: "Kudin da ake aikiwa gida ya kasance ginshikin hanyar samun kudin shiga a Afirka. Yana taimakon iyalai samun na abinci, da kiwon lafiya da bukatun yau da kullum. Idan aka daina samu, haka ya nuna galibin iyalai za su tsunduma cikin talauci.'' Ita kanta Afirka tana bukatar makuden kudin fita daga wannan annoba ta coronavirus wadda ke ci gaba da haifar mata da karin wasu matsalolin.