Corona: Kila a fara aiki daga gida a Jamus
November 14, 2021Sake dawo da dokar aiki daga gida bayan dageta a watan Yulin da ya gabata dai ya biyo bayan sake fuskantar annobar da kasar ke yi a karo na hudu.
Tun a watan Octoban da ya gabata ne dai aka fara samun yawan masu kamuwa da kuma mutuwa sandiyar cutar, lamarin da ake ganin na da nasaba da yadda wadanda ba su yi rigakafinta ba ke yadata tsakanin masu hatsarin kamuwa da cutar.
Ana dai ganin karkashin wannan kuduri, Jamus za ta tilastawa ma'aikata yin aiki daga gida a lokutan da babu tsananin bukatar shiga ofis. Gwamnatin kasar na kuma shirin fara takaita wasu taruka ga wadanda suka yi allurar rigakafin cutar kawai tare da nuna shaidar gwajin cutar.
Tuni dai aka fara tuntubar jam'iyyu da ke kokarin kafa sabuwar gwamnati a kasar wanda za su gabatar da kudurin gaban majalisar dokokin kasar ta Bundestag don neman amincewa.