1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Kasashe za su dandana kuda

October 7, 2020

Bankin duniya ya ce wasu miliyoyin mutane za su dandani kudarsu cikin watanni masu zuwa, saboda matsalolin tattalin arziki da annobar corona ta haddasa wa kasashensu.

https://p.dw.com/p/3jaVe
USA Gebäude der Weltbank in Washington
Hoto: Imago/robertharding/M. Chivers

A wani rahoton da ya fitar a wannan Larabar, Bankin duniya ya ce akwai yiwuwar mutum miliyan 150 za su shiga cikin tsayanin yanayi na fatara a wasu kasashen duniya, inda za su rika rayuwa a kan kasa da dala daya da centi 90 a kowace rana nan da karshen shekarar da ke tafe.

Kashi 82% na miliyoyin mutanen da za su dandana kudarsu saboda karuwar fatarar dai a cewar Bankin na duniya suna kasashen Indiya ne da Najeriya da kuma kasar Indonesiya, kuma galibin su mutane ne da ke zaune a manyan garuruwa.

Bankin wanda ya alakanta hakan da matsalolin da annobar corona ta haddasa wa kasashen, ya ce tsananin zai dogara ne da yadda annobar ta shafi yankuna.