Hadarin kamuwa da corona a Jamus
November 3, 2021A cewar ministan kiwon lafiya na Jamus din Jens Spahn a yanzu corona ta kasance annoba ga wadanda ba a yi wa allurar riga-kafin ba a Jamus. Spahn ya nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar masu zuwa asibitoci kan cutukan da ke da nasaba da annobar coronavirus, annobar da ya ce ba a kawo karshenta a kasar ba. Kalaman nasa dai na zuwa ne, biyo bayan samun karuwar masu dauke da coronan a dakin ajiye wadanda ke cikin matsanancin hali a asibitocin wasu yankunan kasar ta Jamus. Spahn ya maimata kiransa na bukatar a yi allurar karo na uku, musamman ga wadanda ke da shekaru sama da 60. Rahotanni sun nunar da cewa, mutane 194 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar coronan cikin sa'o'i 24 da suka gabata. Wannan dai na zaman karo na farko cikin sama da makonni 114.