1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kammala digiri da sana'ar fige kaji

Muhammad Waziri Aliyu LMJ
June 26, 2019

Wani matashi a jihar Bauchi da ya rungumi sana’ar fige kaji, ya bayyana cewa sana’ar ta masa rana saboda da ita ya dauki nauyin karatunsa har ya kamala jami’a ba tare da wani ya tallafa masa ba.

https://p.dw.com/p/3L6oE
Hahn und Hühner
Sana'ar fige kaji ta tallafawa matashin a harkar karatunsaHoto: Imago/Blickwinkel

Matashin mai suna Bashir Abdullahi, yanzu haka yana gudanar da hidimar kasa biyo bayan kamala karatunsa da ya yi a jami’a. Ya kuma bayyana cewa domin gujewa mutuwar zuciya yasa ya kama wannan sana’a ta figar kaji tun yana karami kasancewar ya taso ya taras iyayensa ba masu karfi bane don haka ya nemi mafita ta hanyar rungumar sana’ar hannu bibbiyu.

Ko ta yaya Bashir har ya samu damar da ya dauki dawainiyar karatun nasa a cikin wannan sana’a bisa la’akari da yadda yanayin samun yake. "Sana'ar ce ginshikin samun ilimina,..... da sana'ar na kammala diploma na yi digiri a yanzu ina hidimar kasa, kuma zan dora zuwa digiri na biyu. Na cimma nasarori sosai inda na mallaki gidan kaina bayan kammala karatu kuma a yanzu haka ina daukar nauyin iyayena."

Ko akwai wani abinda ke zama tarnaki ga Bashir a wannan sana’ar tasa? "Ina fuskantar kalubale kasancewar wasu mutane kan yi min dariya wai nawa nake samu a figar kaji?......Ina kira ga mutane da su daina girman kai su kama sana'a saboda tana da muhimmanci. ......Ko yanzu na samu aikin gwamnati sai na kara yin tunani a kai, ba wai ba na sha'awar aikin ba ne amma gaskiya sai na yi tunan mai zurfi akai."