Somaliya za ta yi bincken harin Al-Shabab
August 22, 2022Talla
Firaminista Hamza Abdi Barre na kasar Somaliya ya yi alkawarin gwamnati za ta tabbatar da adalci kan binciken harin ta'addaci na kungiyar Al-Shabaab mai ikirarin jihadi ta kai na mamaye wani otel da ke birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar.
Firaminista ya nemi 'yan kasar su hada kan wajen kawar da tsagerun kungiyar ta Al-Shabaab masu dangantaka da Al-Qaeda wadda ta kwashe shekara da shekaru suna tayar da kayar baya. Mutane fiye da 20 suka mutu sakamakon harin wannan wasu fiye da kusan 120 suka jikata, kafin daga bisani 'yan sanda suka kusta wajen kawo karshen mamaya na tsagerun.
Wannan harin ke zama mafi muni da kungiyar ta kai tun lokacin da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na Somaliya ya dauki madafun iko a watan Mayu.