Cikas game da warware rikicin Libiya
February 24, 2020Talla
'Yan majalisar wanda galibinsu suka fito daga gabashin kasar sun ce ba za su shiga wannan tattaunawa ba kasancewar Majalisar Dinkin Duniya ba ta amince da jerin sunayen wakilansu da mika don shiga tattaunawar ba.
A ranar Larabar da ke tafe ce dai aka tsara yin wannan zama sai dai ga alama hakan ba za ta faru ba duba da irin matsayin da 'yan majalisar na bangaren Khalifa Haftar din suka dauka.
Wannan dai ba karamin koma baya bane ga yunkurin da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na ganin an kawo karshen tada kayar bayan da Janar Haftar din da dakarunsa ke yi na ganin sun karbe iko da Tripoli babban birnin kasar.